(ABNA24.com) An nuna wannan sabon makami mai linzamin na kariya kirar cikin gida ne a wani taro da aka gudanar a yau Alhamis na zagayowar ranar kera makaman kariya na kasa, sabon makamin mai linzami samfarin bavar 373 yana da karfin da yafi makami mai linzami samfarin S300 na kasar Rasha , kuma yana da karfin kai hari a wuri mai nisan kilomita 27 ta sama da kuma kilo mita 300 a kasa kuma yana da karfin kai hare-hare a wurare masu yawa a lokaci guda.
Kuma wannan makamin kwararrun kasar ne suka yi shi a cikin gida , wanda wannan yasa Iran ta zama ita ce ta 6 a duniya a wannan bangaren.
Ana shi bangaren shugaban kasar Iran Hassan Ruhanida yake bayani a lokacin da yake zagayawa wajen bukin bajen kolin sabon makamin ya nuna cewa: duk da takunkumin zalunci da makiya suka kakabawa Iran da ya hanata samu makamin kariya na sararin samaniya na zamani, amma sabon makamin mai linzami na kasar da kwararrun kasar Iran suka kera acikin gida ya nuna irin karfin da kasar take dashi ne wajen iya tunkarar duk wata barazana.
/129